У нас вы можете посмотреть бесплатно YADDA AKE HADAWA KAJI ORGANIC MULTI-VITAMIN DA GANYEN ZOGALE или скачать в максимальном доступном качестве, видео которое было загружено на ютуб. Для загрузки выберите вариант из формы ниже:
Если кнопки скачивания не
загрузились
НАЖМИТЕ ЗДЕСЬ или обновите страницу
Если возникают проблемы со скачиванием видео, пожалуйста напишите в поддержку по адресу внизу
страницы.
Спасибо за использование сервиса ClipSaver.ru
Ilimin Noma da Kiwo BAYANAI CIKIN HAUSA Dabarun Kiwo Zalla Kiwon Lafiya a Noma/Kiwo YADDA AKE HADAWA TSUNTSAYE MULTI- VITAMIN DA GANYEN ZOGALE iliminnomadakiwoAugust 2, 20221  YADDA AKE HADAWA TSUNTSAYE MULTI- VITAMIN DA GANYEN ZOGALE A baya Kamar yadda na bayyana a kowane sashe na ganyen zogale na lode da sinadaran vitamin masu yawa. Na bayyana sinadara a matsayin wadanda suke habaka jikin tsuntsaye da dabbobi wajen kiwon lafiya tare da daidaita yanayin jiki musamman a kaji. Kamar yadda bincike ya nuna a jikin ganyen zogale kadai akwai Vitamin masu matukar yawa kamar Vitamin A (Alpha & Beta Carotene), B, B1, B2, B3, B5, B6, B12, C, D, E, K, Folic Acid da Biotin.Sannan akwai sinadarai na musamman irin su Calcium, Chloride, Chromium, Copper, Flourine, Iron, Manganese, Magnesium, Molybdenum, Phosphorus, Potassium, Sodium, Selenium, Sulfur, Zinc. Haka kuma a jikinsa akwai sinadaran da ake kira amino acids (masu gudanar da tafiyar tsarin jikin halitta cikin daidaito wajen kara girma da kara nauyi). Irinsu sune Isoleucine, Leucine, Lysine, Methionine, Phenylalanine, Threonine, Tryptophan, and Valine. Hakazalika akwai karin wasu goma (10) irinsu Alanine, Arganine, Aspartic Acid, Cystine, Glutamine, Glycine, Histidine, Proline, Serine, Tyrosine. Dadi da kari iya ganyen zogale yana dauke da karin abubuwa masu nagarta wajen kiwon lafiya irinsu Chlorophyll, Carotenoids, Cytokins, Flavonoids, Plant Sterols, Polyphenols, Lutein, Xanthins, da Rutin. Wadannan tarin sinadarai kadai sun isa su saka a kira ganyen wannan itace shakundum wajen kiwon lafiyar kaji. Cikin wadannan Vitamin akwai vitamin C,D,E, da K da kaji ke matukar bukata wajen kiwon lafiyarsu. Idan muka dauki Vitamin; Vitamin C yana maganin haki a tsuntsaye,kasala,mura, da karawa musu garkuwar jiki musamman kaji. Vitamin D yana maganin shanyewar jikin kaji,rashin karfin kashi,kasa taka kafar kaji,kara girma, da karfin bawon kwai na kowane tsuntsu. Vitamin E da K suna bada kariya wajen cutar nadewar wuyan kaji. A wannan bidiyo zaku sami bayanin yadda ake hada multivitamin nagargajiya mai kyau wanda zaku iya baiwa kajinku da sauran tsuntsayen da kuke kiwo. Sai ku biyo mu....... #broilerchicks #hausa #farming #moringa #mubarakeey #nigeria #kano #nomad #organicfarming #multivitamin #kajinhausa