У нас вы можете посмотреть бесплатно Yelwa United ta lashe Kofin tunawa da Ekene bayan doke Sabo Gunners 6-5 a wasan karshe. или скачать в максимальном доступном качестве, видео которое было загружено на ютуб. Для загрузки выберите вариант из формы ниже:
Если кнопки скачивания не
загрузились
НАЖМИТЕ ЗДЕСЬ или обновите страницу
Если возникают проблемы со скачиванием видео, пожалуйста напишите в поддержку по адресу внизу
страницы.
Спасибо за использование сервиса ClipSaver.ru
Kungiyar kwallon kafa ta Yelwa United ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na tunawa da marigayi Ekene Abubakar Adams na shekara ta 2025. Wasan karshen wanda ya gudana a filin waa na yelwa mini, kungiyar yelwa United ce ta samu nasarar doke Sobo gunners a bugun daga kai sai mai tsaran raga da ci 6 da biyar bayan da aka tashi wasan 2 da 2. Kafin wasan karshen, kungiyar kwallon kakafa ta Kujama FC ta samu nasara akan AG barde FC da ci 2 da 1 inda ta kammala a matsayin ta uku a gasar. A lokacin wasan alkalin wasa, Istifanus Madugu ya bada umurnin ayi shiru na minti daya domin girmama maraigayi Ekene Adams da kuma yar uwa ga wanda ya shirya gasar wacce ta rasu a juma’ar data gabata. Da yake suke jawabi bayan wasan, shugaban hukumar kwallon kafa na jihar kadun, Faisal Muhammad Abdullahi da shugaban kungiyar tuntuba na masuruwa na arewa, Alhaji Shetima yerima sun bayyana marigayi Ekene Adams a matsayin wanda ya kawo gagarumin ci gaba a bangaren wasanni kafin rasuwarsa. Shima da yake jawabi, wanda ya shirya gasar, Engineer Sunday Haruna y ace makasudin shirya gasar shine don tunawa da irin abubuwan ci gaba da marigayi Ekene ya kawo musanman ma a bangaren wasanni. An gabatar da kyautuna ga wasu manyan mutane yayin da kuma zakarun gasar yelwa United suka tafi gida da kofi da naira dubu dari sai ta biyu Sabo gunners suka samu kyautuka tare da kudi yayin da itama Kujama data zo ta uku ta je gida da kofi da kuma kyautuka daban daban. Daga cikin manya baki da suka halarci wasan sun hada da kwamishinan wasanni na jihar kaduna, farfesa Benjamin kumai Guggong da shugaban kumgiyar marubuta wasanni na kasa, comrade Benjamin Isaiah da Benjamin Omale da tsohon yan wasan super eagles Garba Lawal da ishaya jatau da Tajudeen oyekanmi da kuma yar wasan tsakiyar super falcons da suka lashe gasar cin kofin mata na afirika, Halimat Ayinde da dai sauransu.