• ClipSaver
ClipSaver
Русские видео
  • Смешные видео
  • Приколы
  • Обзоры
  • Новости
  • Тесты
  • Спорт
  • Любовь
  • Музыка
  • Разное
Сейчас в тренде
  • Фейгин лайф
  • Три кота
  • Самвел адамян
  • А4 ютуб
  • скачать бит
  • гитара с нуля
Иностранные видео
  • Funny Babies
  • Funny Sports
  • Funny Animals
  • Funny Pranks
  • Funny Magic
  • Funny Vines
  • Funny Virals
  • Funny K-Pop

'Yadda ciwon sikila ya hana ni cimma burina na aure' скачать в хорошем качестве

'Yadda ciwon sikila ya hana ni cimma burina na aure' 5 лет назад

скачать видео

скачать mp3

скачать mp4

поделиться

телефон с камерой

телефон с видео

бесплатно

загрузить,

Не удается загрузить Youtube-плеер. Проверьте блокировку Youtube в вашей сети.
Повторяем попытку...
'Yadda ciwon sikila ya hana ni cimma burina na aure'
  • Поделиться ВК
  • Поделиться в ОК
  •  
  •  


Скачать видео с ютуб по ссылке или смотреть без блокировок на сайте: 'Yadda ciwon sikila ya hana ni cimma burina na aure' в качестве 4k

У нас вы можете посмотреть бесплатно 'Yadda ciwon sikila ya hana ni cimma burina na aure' или скачать в максимальном доступном качестве, видео которое было загружено на ютуб. Для загрузки выберите вариант из формы ниже:

  • Информация по загрузке:

Скачать mp3 с ютуба отдельным файлом. Бесплатный рингтон 'Yadda ciwon sikila ya hana ni cimma burina na aure' в формате MP3:


Если кнопки скачивания не загрузились НАЖМИТЕ ЗДЕСЬ или обновите страницу
Если возникают проблемы со скачиванием видео, пожалуйста напишите в поддержку по адресу внизу страницы.
Спасибо за использование сервиса ClipSaver.ru



'Yadda ciwon sikila ya hana ni cimma burina na aure'

dan ka kalli Aisha, wata matashiya mai shekara 28 da haihuwa, ba ta da wani bambanci da sauran matasa mata da ke harkokinsu na yau da kullum. Ma'aikaciyar gwamnati ce a daya daga cikin biranen arewacin Najeriya; ga ta son-kowa-kin-wanda-ya-rasa kuma kamar sauran mata da suka kai shekarunta, tana da burin yin aure ta hayayyafa. Ma'ana, a wajenta—kamar yadda lamarin yake a wajen matasa maza da mata a tsakanin al'ummomi da dama a sassa daban-daban na nahiyar Afirka—aure muhimmin lamari ne. Sai dai kuma har yanzu hakarta ba ta cimma ruwa ba, saboda samari bila adadin sun fito suna so su aure ta, amma da sun ji larurar da take fama da ita sai su cika rigarsu da iska. Tana fama ne da larurar amosanin jini, wato sikila. "Na tsinci kaina a wani yanayi [da nake ji kamar] ba ni da wani amfani a duniya—idan har zan ci gaba da rayuwa ba tare da na samu [abokin zama] ba, rayuwata ba ta da amfani", inji Aisha. Aisha ce ta uku a jerin yara biyar da aka haifa a gidansu, kuma uku daga cikin 'yan uwan nata ma na dauke da larurar ta amosanin jini. Sai dai daya daga cikinsu ya riga mu gidan gaskiya shekaru kadan da suka gabata. Mahaifiyarsu ma, wacce yanzu shekarunta 60 da haihuwa, ta yi fama da cutar tana karama. Sau da dama dai lalurar kan yi dabaibayi ga rayuwar masu fama da ita ta fannoni da dama, har ma ta kan janyo masu kyama da tsangwama, ko tsana, hatta ma daga danginsu. Mai yiwuwa wannan kyama ce ma ta hana Aisha cimma burinta na ganin wata rana tana rike da danta na cikinta. "Wadanda na sa ran zan aura suna da dan yawa, amma abin bai yiwu ba.'' Wadanda na sa ran zan aura suna da dan yawa, amma abin bai yiwu ba Aisha Bello Yusuf, Mai fama da ciwon sikila "Sau da dama idan manemana sun zo idan na fada masu gaskiya cewa ina dauke da ciwon sikila, su kan yi tunanin ba za su iya aure na ba". Ba Aisha da 'yan uwanta ne kadai ke fama da wannan wahala ba: wata kididdiga da masu fafutukar wayar da kan al'umma game da ciwon sikila suka fitar ta nuna cewa a Najeriya, kimanin yara 150,000 ake haifa a kowace shekara da lalurar, wato kimanin rabin wadanda ake haifa da ita ke nan kowace shekara a fadin duniya. Sai dai kuma cutar ta fi addabar al'umma a kasashen nahiyar Afirka, inda takan shafi kashi biyar cikin 100 na yaran da ake haifa.

Comments

Контактный email для правообладателей: [email protected] © 2017 - 2025

Отказ от ответственности - Disclaimer Правообладателям - DMCA Условия использования сайта - TOS



Карта сайта 1 Карта сайта 2 Карта сайта 3 Карта сайта 4 Карта сайта 5